Da mala’iku suka tafi daga gare su suka koma Sama, sai makiyayan suka ce wa juna, Mu tafi Baitalami yanzu, mu ga abin nan da ya faru, wanda Ubangiji ya sanar da mu. Sai suka tafi da hanzari, suka sami Maryamu da Yusufu, da kuma jaririn a kwance cikin kwamin dabbobi.@Luka 2:15-16

John F. Wade, circa 1743 (Adeste, Fideles).

🔊 pdf nwc.

Jama’ar Ɗan Allah, Ku Taru ku yi murna,
Ku taru, ku taru a Baitalahmi.
Zo mu gaishe shi, Sarkin mala’iku.

Korus

Mu yi masa sujada, mu yi masa sujada,
Mu yi masa sujada, Mai Centonmu.

Zo dai ku gan shi, jariri marar ƙarfi,
Yesu Ɗan Allah ne Madauwami.
Aka haife shi, ba a halicce shi ba.

Korus

Rundunan Sama, yi ta rera waƙa,
Can cikin Sama ku ke yabonsa,
Yabo ga Allah, yabo kuwa ga Ɗansa.

Korus

I, Ubangiji, kai ne mu ke yabo
Gaisuwa mai gaskiya mu ke yi maka.
Kai, Kalmar Allah, cike da alheri.

Korus