Ba labari sai ga taron rundunar Sama tare da mala’ikan nan, suna yabon Allah, suna cewa, Ɗaukaka ga Allah ta tabbata, a can cikin Sama mafi ɗaukaka. A duniya salama ta tabbata, ga mutanen da yake murna da su matuƙa.@Luka 2:13-14
portrait
James Montgomery (1771-1854)

James Montgomery, 1816.

Henry T. Smart, 1867 (🔊 pdf nwc).

portrait
Henry T. Smart (1813-1879)

Daa, mala’iku ke shaidar
Haihuwar Yesu Mai Ceto.
Ji labarin farinciki
Wanda shi ke dominku.

Korus

Zo, ku yi masa sujada
Shi Sarkin Sarakuna.

Makiyaya suna tsaron
Garkensu da daren nan.
Haske ne ya kewaye su,
Aka shaida musu ma.

Korus

Masu hikima na duniya
Bar zurfin tunaninku
Nemi ceto wurin Yesu,
Kuna jin labarinsa.

Korus

Sarakuna, talakawa
Malamai, almajirai
Mazaje da mata duka,
Tsofaffi da jarirai.

Korus